Kamfanin dillancin labarai na ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; daga ranar sha uku zuwa sha bakwai ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Nairobi fadar mulkin kasar Keniya za a gudanar da kasuwar baje koli kan rawar da fasaha ke takawa a cikin kur'ani mai girma.Wannan kasuwar baje kolin za a gudanar da ita ne tare da hadin guiwar cibiyar da ke kula da hubbarin imam Rida (AS) kuma za a nuna akalla hotuna arba'in na fasaha da suka shafi kur'ani a karni na uku ya zuwa yanzu da kuma mu'assishi da daman e za su samu halartar wannan kasuwar baje koli ta birnin Nairobi fadar mulkin kasar Keniya.
798249