Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a karo na sha shidda komitin zartarwa ba jami'o'in musulunci a duniya a ranar hudu ga watan khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya gudanar da taronsa a birnin Dubai na hadeddiyar daular larabawa. Wannan taro da komitin zartarwa na jami'o'in musulunci ya gudanar yana karkashin kungiyar da ke kula da harkokin al'adu da ilimi a karkashin kungiyar hadin kan kasashen musulmi Asseco inda aka samu halartar shugabannin jami'oi day an jami'a da kuma wadada harkokin ilimi ya shafa a wannan taro na birnin Dubai.
799033