Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar al’alam an bayyana cewa, mutanen kasar Bahrain sun fara gudanar da gangamin makon kare juyin juya halinsu na neman sauyi daga tsarin mulukiya na kama karya da danniyar masarautar kasar, insa matasa za su fara gudanar da zanga-zanga a cikin sassa na kasar a wannan mako da muke ciki.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muzn an bayyana cewa, an dage gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasar Bahrain mai taken zikrull hakim da ake gudanarwa duk shekara a kasar, sakamakon abubuwan da suke faruwa a halin yanzu na cin zarafin al’ummar muslmi da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da suka yi, tare da hadin gwiwa da gwamnatin wahabiyawan saudiyya.
Daya daga cikin manyan malaman addini na kasar Bahrain Abdulkarin Abduljalil ya bayyana cewa, mutanen kasar Bahrain sun mabiya mazhabar shi’a da ‘yan sunna na kasar sun rayu tsawon shekaru a kasar ba tare da wata matsala ba, amma a lokacin da suka fara bore domin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar sai gidana sarauta mayar da maganar ta mazhabanci domin samun damar murkushe masu bore a fadin kasar.
Malamin ya ci gaba da cewa babu wani dalili da zai sanya mahukuntan Bahrain su fake da batun mazhaba domin murkushe masu gudanar da zanga-zangar neman sauyi na siyasa akasar, tare da tabbatar da tsarin kama karya kansu, domin kuwa kowa aduniya ya san abin da ke faruwa ba shi da wata dangantaka da batun mazhaba kamar yadda gidanasarautar da masu kare daga kasashen larabawa suke rayawa.
Al’ummar kasar Bahrain mabiya mazhabar shi’a da ‘yan sunna na kasar sun rayu tsawon shekaru a kasar ba tare da wata matsala ba, amma a lokacin da suka fara bore domin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar sai gidana sarauta mayar da maganar ta mazhabanci domin samun damar murkushe masu zanga-zanga.
800218