Bangaren kas ada kasa, an fara gudanar da wani taron baje koli na kayyakin fasahar muslunci guda 1001 a babban ginin cibiyar bunkasa harkokin ilimi da ala’adu ta jahar California da ke birnin Los Angeles, da ke samun halartar masana da mabiya addinin muslunci na jahar da wasu jahohin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na islam Online an bayyana cewa, an fara gudanar da wani taron baje koli na kayyakin fasahar muslunci guda 1001 a babban ginin cibiyar bunkasa harkokin ilimi da ala’adu ta jahar California da ke birnin Los Angeles, da ke samun halartar masana da mabiya addinin muslunci na jahar da wasu jahohin kasar ta Amurka.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba.
Gudanar da sallar juma’a abirnin Rom fadar mulkin kasar Italia a babban dandalin da ke tsakiyar birnin, domin nuna rashin amincewa da matakin da mahukuntan suka dauka na kin bayar da izinin gina masallaci a birnin, na tattare da babban sako.
800081