Bangaren siyasa da zamantakewa: Rashid Alganusi shugaban kungiyar gwagwarmaya ta musulunci a jamhuriyar Tunisiya a wani gagaramin taron da magoya bayansa suka shirya a wannan kasar ya bukaci kafa wata uwan jam'iya dahada kowa guri guda kama daga jam'iyu da kungiyoyi domin kare juyin juya halin sauyi da al'ummar suka suka yi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Rashid Alganusi shugaban kungiyar gwagwarmaya ta musulunci a jamhuriyar Tunisiya a wani gagaramin taron da magoya bayansa suka shirya a wannan kasar ya bukaci kafa wata uwan jam'iya dahada kowa guri guda kama daga jam'iyu da kungiyoyi domin kare juyin juya halin sauyi da al'ummar suka suka yi.Alganusi ya fadi haka da kuma gabatar da wannan bukata a daidai lokacin da ake yada jita jitar jinkirta zaben majalisar dokokin a kasar a wani kokari da kasar ke yin a komawa kan tafarkin demokradiya bayan kifar da gwamnatin Zainul abidina dan kama karaya da cewa: dole a gudanar da zabe a kasar cikin gaggauwa domin hakan ne zai maido da tsaro da kwanciyar hankali a kasar.
801476