Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani dadaddun kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki a kasar Yemen, wanda ma’aikatar kula da harkokin al’adu da bunkasa ilmomi da harkar bincike ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wannan mako.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo marebpress cewa, an gudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani dadaddun kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki a kasar Yemen, wanda ma’aikatar kula da harkokin al’adu da bunkasa ilmomi da harkar bincike ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wannan mako, wanda aka kammala a jiya.
Kasar Yemen dai tana daya daga cikin kasashen larabawa da suke da dadadden tarihin musulunci, wanda hakan ne ma ya sanya aka samu da dama daga cikin abubuwan tarihin muslunci a kasar, wanda hakan ke komawa zuwa ga shekaru sama da dubu daya da wani abu da suka gabata.
Gudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani dadaddun kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki a kasar Yemen, wanda ma’aikatar kula da harkokin al’adu da bunkasa ilmomi da harkar bincike ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wannan mako, wanda hakan yake da babban tasiri a harkar bunkasa al’adu na kasar da ma tarihin musulunci.
801548