IQNA

An Fara Gudanar Da Zaman Taron Tunawa Da Marigayi Imam Khomeini (RA) A Tehran

12:50 - June 02, 2011
Lambar Labari: 2132752
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da zaman taron tunawa da jagoran juyin juya halin musunci na Iran marigayi Imam Khomeini a birnin Tehran, wanda ke samun halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen duniya, musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yar gizo an bayyana cewa, an fara gudanar da zaman taron tunawa da jagoran juyin juya halin musunci na Iran marigayi Imam Khomeini a birnin Tehran, wanda ke samun halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen duniya, musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi da ma wasu kasashen yammacin turai.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo na ashirin da biyu da ake gudanar da irin wannan taro a birnin Tehran, muhimman abubuwan da aka fi mayar da hankali kansu a lokacin gudanar da taron shi ne, bayani kan irin gudunmawar da ya bayawa wajen fadakar al'ummar musulmi a bangarori daban-daban na rayuwa, da kuma yadda ya kamata su yi riko da koyarwar addinin Allah madaukakin sarki.

An fara gudanar da zaman taron tunawa da jagoran juyin juya halin musunci na Iran marigayi Imam Khomeini a birnin Tehran, wanda ke samun halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen duniya, musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi.

802225

captcha