IQNA

Za A Tattara Kwafi-Kwafi Na Kur'anai Da Aka Buga Da Kuskure A Palastinu

13:40 - June 08, 2011
Lambar Labari: 2134953
Bangareb kasa da kasa, za a tattara kur'anai da aka buga da kuskure a cikinsu a palastinu, domin kaucewa karanta su a yadda aka buga su, musamman ma wadanda aka samu kurakurai a ckinsu a surorinsa masu tsarki.Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Anam ta kasar Bahrain an bayyana cewa, za a tattara kur'anai da aka buga da kuskure a cikinsu a palastinu, domin kaucewa karanta su a yadda aka buga su, musamman ma wadanda aka samu kurakurai a ckinsu a surorinsa masu tsarki, wadanda aka buga domin yin amfani da su a cikin watan ramadana mai zuwa.

A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nasij an bayyana cewa, za a fara gudanar da wani zaman taro na bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya, wadda ta kebanci mata 'yan makarantun sakadandare na kasar, a babban dakin taruka na katafaren otel din nan na Kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa a wannan zaman taro za a horar da yaran ne kan muhimman hanyoyin koyon harda, inda suka hada da karatun da kuma tajwidi, inda malamai daga cikin makaranta da kuma wasu daga cikin alkalan da suka saba jagorancin gasar kur'ani ta kasa da kasa.

804634


captcha