IQNA

Musulmin Birtaniya Sun Nuna Damuwa Kan Karuwar Kymar Mabiya Musulunci A Kasar

18:31 - June 09, 2011
Lambar Labari: 2135411
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci na kasar Birtaniya kuma mabobi a majalisar koli ta musulmin kasar sun nuna matukar damuwa dangane da yadda kyamar mabiya addinin muslunci ke ci gab ada karuwar kasar, musamman ma acikin wadannan lokuta.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlasinfo an bayyana cewa, mabiya addinin muslunci na kasar Birtaniya kuma mabobi a majalisar koli ta musulmin kasar sun nuna matukar damuwa dangane da yadda kyamar mabiya addinin muslunci ke ci gab ada karuwar kasar, musamman ma acikin wadannan lokuta da kamfe kan addinin musuluncike ta karuwa acikin kasashen yammacin turai.
Wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cm-life an bayyana cewa, za agudanar da wani zaman taro na yin nazari kan fasahohin muslunci na zamani, wanda aka shirya gudanarwa jami’ar Machigan, da jami’an gami malamai daga jami’ar d akuma wasu jami’oin kasar Birtaniya za su samu halarta, da ma wasu kasashen ketare.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba.
805345
captcha