IQNA

Fadar Vatican Za Ta Shirya Zaman Tattaunawa Tsakanin Mabiya Addinai

15:22 - June 13, 2011
Lambar Labari: 2137565
Bangaren kasa da kasa, fadar Vatican ta mabiya addinin kirista da ke birnin Rom na kasar Italia za ta shirya gudanar da wani zaman taro na tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, wanda zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka hada dukkanin bangarorin ta yadda za a kara samun fahimtar juna.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na lebanonfiles an bayyana cewa, fadar Vatican ta mabiya addinin kirista da ke birnin Rom na kasar Italia za ta shiya gudanar da wani zaman taro na tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, wanda zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka hada dukkanin bangarorin ta yadda za a kara samun fahimtar juna tsakaninsu.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daga cikin ayyukan da fadar vatican ta saba shiryawa tun lokacin tsohon paparoma na biyu, wanda ya sa hakan ya zama wani zaman taro na shekara-shekara da ta saba gudanarwa, tare da halartar masana da malamai daga sassa daban-daban na kasashen duniya, da suka hada kasashen larabawa da na musulmi.
Fadar Vatican ta mabiya addinin kirista da ke birnin Rom na kasar Italia za ta shiya gudanar da wani zaman taro na tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, wanda zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka hada dukkanin bangarorin ta yadda za a kara samun fahimtar juna.
807263


captcha