IQNA

Zaman Taro A Karo Na Farko Kan Harkokin Bankin Muslunci A Kasar Oman

21:03 - June 16, 2011
Lambar Labari: 2139201
Bangaren kasa da kasa, za agudanar da zaman taro kan harkokin bankin musulunci a karon farko a kasar Oman, tare da halartar masana kan harkokin banki da harkokin kudi na kasa da kasa, wanda za a gudanar a birnin Maskat fadar mulkin kasar ta Oman.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Zawya an bayyana cewa, za agudanar da zaman taro kan harkokin bankin musulunci a karon farko a kasar Oman, tare da halartar masana kan harkokin banki da harkokin kudi na kasa da kasa, wanda za a gudanar a birnin Maskat fadar mulkin kasar.
Wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na Bernama cewa, pira ministan kasar Malazia ya jaddada muhimmancin gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron bude gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar ta Malazia.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na lebanonfiles an bayyana cewa, fadar Vatican ta mabiya addinin kirista da ke birnin Rom na kasar Italia za ta shiya gudanar da wani zaman taro na tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, wanda zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka hada dukkanin bangarorin ta yadda za a kara samun fahimtar juna tsakaninsu.
809392


captcha