Bangaren kasa da kasa, an sanar da sunayen wadanda za su shiga gasar karatun kur’ani tare da tajwidinsa akasar Oman, wanda za a fara gudanarwa a cikin wannan wata, tare da halartar malamai da kuma wasu wakilan cibiyoyin ilimi da makarantun muslunci gami wakilan ma’akatar kula da aharkokin addini.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, an sanar da sunayen wadanda za su shiga gasar karatun kur’ani tare da tajwidinsa akasar Oman, wanda za a fara gudanarwa a cikin wannan wata, tare da halartar malamai da kuma wasu wakilan cibiyoyin ilimi da makarantun muslunci gami wakilan ma’akatar kula da aharkokin addini a kasar ta Oman, kuma gasar za abude ta ne a birnin Maskat fadar mulkin kasar.
A bangare guda kuma wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ra’y an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani kan mu’ujizar kur’ani mai tsarki da kuma adabi a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin ilimi da adabin musulunci ta kasa da kasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin na Aman.
A wani rahoton kuma an bayyana cewa a wani labari da aka nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na middle East Monitor cewa, ana shirin bude hanyoyin karkashin kasa da yahudawan sahyuniya suka gina karkashin masallacin Qods mai alfarma, a lokacin da al’ummomin duniya gami da shugabannin larabawa suka yi gum da bakinsu kan wannan tabargaza ta yahudawan sahyuniya a wurare masu tsarki na al’ummar musulmi.
Tun bayan da yahudawan sahyuniya suka fara gudanr da wannan aiki, masu ‘yancin siyasa daga cikin kasashen musulmi da kuma ‘yan kadan daga cikin kasashen larabawa, sun nuna rashin amincewarsu da wannan mummanan aiki da ke samun cikakken goyon baya daga gwamnatocin Amurka da munafukan larabawa, musamman ma wadanda suke da dangantaka ta zahiri da haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma masu dangantaka ta bayan fage.
812453