IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Taro Kan Kayan Halal A Karon Farko A Kasar Turkiya

20:30 - June 25, 2011
Lambar Labari: 2144163
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro kan kayan halal a karon farko a birnin Ankaa fadar mulkin kasar Turkiya, tare da halartar masana daga kasashen duniya musamman ma na musulmi da kuma n alarabawa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto wani rahoto daga bangaren yada labarai na bankin muslunci ICB cewa, za a gudanar da wani zaman taro kan kayan halal a karon farko a birnin Ankaa fadar mulkin kasar Turkiya, tare da halartar masana daga kasashen duniya musamman ma na musulmi da kuma na larabawa da ma wasu kasashen Asia.

A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na rasid an bayyana cewa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar saudiyya sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar kasar Bahrain da suke fuskantar zalunci da danniya daga azzaluman sarakunan kasar gami da na kasar Saudiyya, tun daga lokacin da suka fara gudanar da gangamin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar.
A wani labarin kuma makamanicn wannan kungiyar tarayyar turai ta yi kakkausar suka kan hukuncin kisa da kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan wasu matasa da suka shiga zanga-zangar neman sauyi a kasar.
Kakakin kungiyar tarayyar turai ya fadi jiya cewa ko alama ba za su amince da hukuncin kisan da kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan matasan hudu ba, kuma kungiyar tana yin kira ga mahukuntan kasar ta Bahrain ta kawo karshen yin amfani da karfin da take yi kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauyen siyasa a kasar.
814154
captcha