IQNA

Yaki Da Alamomin Shaidana Na Ta’addanci Aiki Ne Da Ya Rataya Kan Kowa Da Kowa

22:11 - June 26, 2011
Lambar Labari: 2144786
Bangaren siyasa, Jaoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, yaki da ta’addanci wajibi ne a kan dukkanin mutane baki daya, jagoran ya sheda hakan ne a cikin wani bayani da aike zuwa ga taron kasa da kasa na yaki da ta’addanci a birnin Tehhran fadar mulkin kasar Iran.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Tehran an bayyana cewa, Jaoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, yaki da ta’addanci wajibi ne a kan dukkanin mutane baki daya, jagoran ya sheda hakan ne a cikin wani bayani da aike zuwa ga taron kasa da kasa na yaki da ta’addanci a birnin Tehhran fadar mulkin kasar Iran tare da halartar shugabannin kasashe shida da kuma shugabannin hukumomi na kasashe daban-daban.
Taron dai an gudanar da shi da nufin bayyana abin da ake kira ta’addanci, tare da banbance ta’addanci da kuma gwagwarmaya, inda mahalarta taron daga kasashe kimanin sittin suka amince kan cewa ta’addanci da ake kira ba ya da dangantaka da kungiyoyin gwagwarmaya, musamman ma wadanda suke yaki da mamayar yahudawan Sahyuniya a palastinu da Lebanon.
Jaoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, yaki da ta’addanci wajibi ne a kan dukkanin mutane baki daya, jagoran ya sheda hakan ne a cikin wani bayani da aike zuwa ga taron kasa da kasa na yaki da ta’addanci a birnin Tehhran fadar mulkin kasar. 814628
captcha