Bangaren kasa da kasa, an bayyana babban malamin kur’ani na kasar Masar da Allah ya yi masa rasuwa amatsayin wani babban abin koyi ga dukkanin malaman kur’ani da dalibansa akasar Masar, domin kuwa ya kafa makarantar kur’ani tare da horar da fitattun makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki da duniyar musulmi take alfahari da su.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, wani makarancin kur’ani daga kasar Masar Anwar Shuhat Muhmamad Anwar ya bayyana babban malamin kur’ani na kasar Masar da Allah ya yi masa rasuwa amatsayin wani babban abin koyi ga dukkanin malaman kur’ani da dalibansa akasar Masar, domin kuwa ya kafa makarantar kur’ani tare da horar da fitattun makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki da duniyar musulmi take alfahari da su, kuma duniyar musulmi ba za ta taba mantawa da gudunmawar da ya bayar ta wannan fuska ba.
Wani labarin kuma aka nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar yaum Sabi ta kasar Masar an bayyana cewa, an gudanar da zaman ta’aziyya na rasuwar babban malamin kur’ani kuma makaranci wato shekhul kurra na kasar Masar, wanda Allah ya yi wa rasuwa kwanaki uku da suka gabata, dukkuwa da cewa manyan malaman Azhar sun kauracewa janazarsa da kuma zaman ta’aziyar tasa.
Da dama daga cikin iyalan mamacin sun nuna matukar mamaki dangane da matakin da malaman jami’ar Azhar suka dauka na kaurace ma janazar shehin malamamin, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa harkokin kur’ani a akasar Masar, wanda ya kafa makarantun da suka samar da fitattun malaman kur’ani da makaranta da duniyar musulmi ke takama da su a halin yanzu a koina cikin kasashen musulmi.
814802