Bangaren kasa da kasa, an fitar da wata mujalla ta mata musulmin palastinu, wadda aka fi sani Palastinu Muslima, da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas take daukar nauyin bugawa da kuma rarrabawa ga palastinawa mata, domin sanin hukunce-hukunce na addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an fitar da wata mujalla ta mata musulmin palastinu, wadda aka fi sani Palastinu Muslima, da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas take daukar nauyin bugawa da kuma rarrabawa ga palastinawa mata, domin sanin hukunce-hukunce na addinin muslunci da kur’ani.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na 20 minutes an bayyan acewa, shafin yanar gizo na faceobok ya shafe wani rubutu da dan gidan pira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi da ke yin batunci ga addinin musulunci, wanda ya jawo rikici mai tsanani da cacar baki tsakanin musulmi da kuma masu kyamar addinin muslunci, musamman ma yahudawan sahyuniya daga cikinsu.
A bangare guda kuma a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na lebanonfiles an bayyana cewa, fadar Vatican ta mabiya addinin kirista da ke birnin Rom na kasar Italia za ta shiya gudanar da wani zaman taro na tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, wanda zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka hada dukkanin bangarorin ta yadda za a kara samun fahimtar juna tsakaninsu.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daga cikin ayyukan da fadar vatican ta saba shiryawa tun lokacin tsohon paparoma na biyu, wanda ya sa hakan ya zama wani zaman taro na shekara-shekara da ta saba gudanarwa, tare da halartar masana da malamai daga sassa daban-daban na kasashen duniya, da suka hada kasashen larabawa da na musulmi.
814981