IQNA

Abin Da Ke Faruwa A Kasar Bahrain Kisan Kiyashi Ne Ake Yi Kan Al’ummar Kasar

21:31 - June 27, 2011
Lambar Labari: 2145421
Bangaren zamantakewa, a wani zaman tattaunawa da aka gudanar kan hakkokin mata da kanan yara da ake tozartawa a kasar Bahrain, lauyoyi da wakilan kungiyoyin kare hakkin bil adama sun amince kan cewa, abin da ke faruwa a kasar kisan kiyashi ne ake yi kan fararen hula masu neman sauyi.
Kamfanin dillancin labarn iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, wani zaman tattaunawa da aka gudanar kan hakkokin mata da kanan yara da ake tozartawa a kasar Bahrain, lauyoyi da wakilan kungiyoyin kare hakkin bil adama sun amince kan cewa, abin da ke faruwa a kasar kisan kiyashi ne ake yi kan fararen hula masu neman sauyi a kasar ta hanyar lumana..
Labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran AFP an bayyana cewa, mutanen kasar Bahrain sun gudanar da gagarumar zanga-zangar yin Allawadai da mahukuntan kasar da suke yin amfani da karfi wajen murkushen boren fararen hula na lumana, tare da dakarun mamaya na kasar Saudiyya, inda suka ci zarafin mutane da keta alfarmar wurare masu tsarki, kamar masallatai da wuraren gudanar da tarukan addini.
A nasa bangaren babban malamin addinin musulunci na kasar ta Bahrain ya bayyana cewa, mahukuntan kasar suna yin kuskure inda suke zaton cewa ta hanyar yin amfani dakarfi da murkushe fararen hula za su iya yin mulki a kasar, ya ce hakan babu abin da zai jawo illa kara rikicewar lamurra a kasar.
Al’ummar kasar Bahrain sun gudanar da gagarumar zanga-zangar yin Allawadai da mahukuntan kasar da suke yin amfani da karfi wajen murkushen boren fararen hula na lumana, tare da dakarun mamaya na kasar Saudiyya, inda suka ci zarafin mutane da keta alfarmar wurare masu tsarki da suka hada masallatai da wuraren tarukan addini a kasar.
815465




captcha