IQNA

Babban Kwamitin Hadin Gwiwa Na Makaranta Kur'ani Zai Gudanar Da Zamansa

17:41 - June 28, 2011
Lambar Labari: 2146053
Bangaren kasa da kasa, babban kwamitin hadin gwiwa tsakanin makaranta kur'ani mai tsarki na kasashen musulmi da na larabawa zai gudanar da babban taronsa na shekara a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi ta kasar Masar an bayyana cewa, babban kwamitin hadin gwiwa tsakanin makaranta kur'ani mai tsarki na kasashen musulmi da na larabawa zai gudanar da babban taronsa na shekara a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar, da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci shirye-shiryen karatukan watan Ramadan.

A labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Ahram da ake bugawa a kasar Masar an bayyana cewa, babban malamin jami'ar Azhar ta kasar Masar Sheikh Ahmad Tayyib ya kira ga dukkanin malaman jami'ar Azhar da sauran malaman addinin muslunci ta kasashen duniya da su yada sahihiyar koyarwar addinin mulunci a duniya.
Babban malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da wani jawabi a gaban wani bababn taro na malaman addinin muslunci na duniya da aka gudanar a birnin Alkahira fadar mulkin kasar ta Masar, wanda ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen duniya, musamman ma kasashen musulmi.
Wannan malamin jami'ar Azhar ta kasar Masar Sheikh Ahmad Tayyib ya kira ga dukkanin malaman jami'ar Azhar da sauran malaman addinin muslunci ta kasashen duniya da su yada sahihiyar koyarwar addinin mulunci a mataki na duniya baki daya.
816058


captcha