IQNA

An Fara Gudanar Da Zaman Taron Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Musulmi

17:17 - June 29, 2011
Lambar Labari: 2146715
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da zaman ministocin harkokin wajen kasashen musulmi a kasar Kazakistan, tare da halartar jami'an gwamnatin kasar, inda za su tattauna muhimman batutuwa da suka danganci harkokin musulmi na cikin gida.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an fara gudanar da zaman ministocin harkokin wajen kasashen musulmi a kasar Kazakistan, tare da halartar jami'an gwamnatin kasar, inda za su tattauna muhimman batutuwa da suka danganci harkokin musulmi na cikin gida, da kuma a matsayi na kasashe.

Kakakin kungiyar tarayyar turai Jerzy Buzek, ya fadi jiya cewa ko alama ba za su amince da hukuncin kisan da kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan matasan hudu ba, kuma kungiyar tana yin kira ga mahukuntan kasar ta Bahrain ta kawo karshen yin amfani da karfin da take yi kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauyen siyasa a kasar.
A jiya ne wata kotun soji da mahukuntan Bahrain suka kafa cikin makwannin suka, ta yanke hukuncin kisa kan wasu matasa hudu, bisa zargin cewa suna da hannu wajen mutuwar 'yan sanda biyu a lokacin gudanar da zanga-zanga a birnin Manama.
Al'ummomin duniya da dama da suka hada da kungiyoyin kare hakkin bil adama, suna ci gaba da yin Alawadai da mahukuntan kasar Bahrain da kuma na Saudiyya, sakamakon yin amfani da karfin soji da suka yi wajen yin kisan gilla a kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa ta hanyar lumamana a cikin kasar. 816591
captcha