Bangaren kasa da kasa, mahardata kur’ani mia tsarki na kasashen yankin Asia ta tsakiya sun gudanar da zaman taronsu a birnin Beshkik na kasar Kazagistan, tare da hadin gwiwa da kwamitin mahardata kur’ani na duniya, da kuma taimakon ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na nasij an bayyana cewa, mahardata kur’ani mia tsarki na kasashen yankin Asia ta tsakiya sun gudanar da zaman taronsu a birnin Beshkik na kasar Kazagistan, tare da hadin gwiwa da kwamitin mahardata kur’ani na duniya, da kuma taimakon ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar.
Ya kuma nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na IFESI an bayyana cewa, an sanar da sabon tsarin harkokin tattalin arzikin musulmin kasar Faransa, da nufin kara bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki na musulmin kasar ta dukkanin bangarori na tattalin arziki.
Wani rahoton kuma ya ce pira ministan gwamnatin rikon kwarya a kasar Tunisia Albaji Kaid Sabisi ya bayyana cewa suna yin matukar kokarinsu domin ganin cewa sun bunkasa ayyukan babban bankin musulunci a kasar, ta yadda zai amfanar da masu son saka hannayen jari da sauran harkokin kasuwanci.
818092