IQNA

An Gudanar Da Janazar Babban Malamin Addinin Muslunci A Yankin Qatif Na Saudiyya

15:11 - July 02, 2011
Lambar Labari: 2147612
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addini Allamah Sheikh Muhammad Taqiy Ma’tuk da Allah ya yi masa rasuwa a yankin Qatif da ke gabacin kasar Saudiyya, an gudanar da janazarsa tare da halartar dubban mumunai a yankin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, babban malamin addini Allamah Sheikh Muhammad Taqiy Ma’tuk da Allah ya yi masa rasuwa a yankin Qatif da ke gabacin kasar Saudiyya, an gudanar da janazarsa tare da halartar dubban mumunai a yankin na Qatif.
A bangare guda kuma an gudanar da zaman ta’aziyya na rasuwar babban malamin kur’ani kuma makaranci wato shekhul kurra na kasar Masar, wanda Allah ya yi wa rasuwa kwanaki uku da suka gabata, dukkuwa da cewa manyan malaman Azhar sun kauracewa janazarsa da kuma zaman ta’aziyar tasa.
Da dama daga cikin iyalan mamacin sun nuna matukar mamaki dangane da matakin da malaman jami’ar Azhar suka dauka na kaurace ma janazar shehin malamamin, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa harkokin kur’ani a akasar Masar, wanda ya kafa makarantun da suka samar da fitattun malaman kur’ani da makaranta da duniyar musulmi ke takama da su.
Babban malamin addini Allamah Sheikh Muhammad Taqiy Ma’tuk da Allah ya yi masa rasuwa a yankin Qatif da ke gabacin kasar Saudiyya, an gudanar da janazarsa tare da halartar dubban mumunai a yankin da ke gabacin kasar Saudiyya. 818061
captcha