IQNA

An Yi Kira Ga Mabiya Mazhabar Iyalan Gidan Manzo Da Rubanya Himma A Tafsirin Kur'ani

19:14 - July 05, 2011
Lambar Labari: 2149590
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin malaman addini kuma mabiyin tafarkin iyalan gidan manzo a kasar India Sayyid Hussain ya yi kira ga dukkanin malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah na duniya da su rubanya himma wajen tafsirin kur'ani mai tsarki.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, daya daga cikin malaman addini kuma mabiyin tafarkin iyalan gidan manzo a kasar India Sayyid Hussain ya yi kira ga dukkanin malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah na duniya da su rubanya himma wajen tafsirin kur'ani mai tsarki bisa la'akari da cewa wannan shi ne abin da zai kara fitar da mahnarsu a duniya.

Malamin ya ci gaba da cewa malaman mabiyar tafrkin ialan gidan manzo suna da gagarumar gudunmawar da za su bayar ta fuskoki da dama, domin ci gaban wannan mazhaba da ma addinin muslunci baki daya ta fuskacin tafsirin kur'ani a mahanagar iyalan gidan manzon Allah, tare fitar da hakan ga duniya.

Daya daga cikin malaman addini kuma mabiyin tafarkin iyalan gidan manzo a kasar India Sayyid Hussain ya yi kira ga dukkanin malaman mazhabar iyalan gidan manzon Allah na duniya da su rubanya himma wajen tafsirin kur'ani mai tsarki. Da ilmominsa.

819151


captcha