IQNA

Kungiyar Hadin Kan Malaman Musulunci Ta Soki Amurka Kan Makirci Ga Musulunci

19:17 - July 05, 2011
Lambar Labari: 2149595
Bangaren siyasa da zamatakewa, a wani babban taron da kungiyar hadin kan malaman muulmin duniya ta gudanar a birnin Islam-abad na kasar Pakistan ta yi kakkausar suka yadda Amurka take kulla makirci ga mabiya adinin Musulunci a ko'ina cikin fadin duniya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, a wani babban taron da kungiyar hadin kan malaman muulmin duniya ta gudanar a birnin Islam-abad na kasar Pakistan ta yi kakkausar suka yadda Amurka take kulla makirci ga mabiya adinin Musulunci a ko'ina cikin fadin duniya baki daya.

A bangare guda kuma ministan tsaron kasar Iran Janar Ahmad Wahidi ya isa birnin Kabul na kasar Afghanistan a wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya fara gudanarwa a kasar.

Ziyarar ta ministan tsaron kasar Iran a Afghanistan ta zo ne a matsayin karba goron gayyata daga takwaransa na kasar ta Sfghanistan Abdulrahim Wardak. Jami'an gwamnatin Afghanistan tare da jakadan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne suka tarbi Janar Wahidi a babban filin safka da tashin jiragen sama na birnin Kabul. A yayyin wannan ziyara zai gana da manayan jami'an gwamnatin kasar Afghanistan kan batutuwa da dama, da suka hada da siyasa, tattalin arziki da kuma tsaro.

Wannan shi ne karon farko da ministan tsaron kasar Iran ya kai ziyarar aiki a kasar Afghanistan, tun bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran a cikin shekara ta 1979. A cikin watan Maris din ya gabata ma ministan harkokin cikin gida na kasar Iran ya kai wata ziyarar aiki a kasar ta Afghanistan.

819229

captcha