IQNA

Tauraron Dan Adam Na Farko Na Bankin Musulunci Zai fara Aiki

11:39 - July 07, 2011
Lambar Labari: 2150390
Bangaren kasa da kasa, ana shirin harba tauraron dan adam na farko na bankin Musulunci mai suna Inayah, wanda ake sa ran a cikin watan Ramadana mai zuwa ne za a kaddamar da shi domin amfanin al'ummar musulmi da sauran al'ummomin duniya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Riyad an bayyana cewa, ana shirin harba tauraron dan adam na farko na bankin Musulunci mai suna Inayah, wanda ake sa ran a cikin watan Ramadana mai zuwa ne za a kaddamar da shi domin amfanin al'ummar musulmi da sauran al'ummomin duniya baki daya, musamman ma wadanda suke da sha'awar yin aiki tare da wannan banki.

Wani jami'in gwamnatin waabiyawan Saudiyya ya bayyana cewa, yanzu haka an riga an sanya hannu kan harba wannan tauraron dan adam, wanda zai rika watsa shirye-shirye da suka shafin harkokin kudi a mahangar muslunc, kuma za a rika watsa shirin ne a cikin yaruka uku, wato harsunan turancin ingilishi, laranci da kuma malayi.

Ana shirin harba tauraron dan adam na farko na bankin Musulunci mai suna Inayah, wanda ake sa ran a cikin watan Ramadana mai zuwa ne za a kaddamar da shi domin amfanin al'ummar musulmi da sauran al'ummomin duniya baki daya.

821124








captcha