Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nasij an bayyana cewa, kimanin kasashen duniya 70 ne suka sanar cewa a shirye suke su halarci gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da za a gudanar a kasar Masar, tare da halartar wakilai daga wasu kasashen musulmi da na larabawa da ma wasu kasashen turai da na Asia.
Wannan labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo an jaridar Qods arabi da ake bugawa a birnin London na kasar Birtaniya an bayyana cewa, kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon ta hizbullah ta yaba da furucin da ya fito daga bakin babban malamin addini na jami'ar Azhar da ke kasar Masar, da ke neman samun fahimtar juna tsakanin mabiya tafarkin sunna da kuma mabiya tafarkin ahlul baiti.
Bayani da kungiyar ta fitar ya zo a lokacin da shehin malamin ya bayyana wa duniyar musulmi cewa 'yan shi'a musulmi ne kamar sauran musulmi, saboda haka babu wani dalili na mayar da su saniyar ware a cikin harkokin Musulunci, a lokacin da wasu mabiya tafarkin wahabiyanci ke ta kokarin fitar da mabiya tafarkin ahlul bait daga addini.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon ta hizbullah ta bayyana furucin da ya fito daga bakin babban malamin addini na jami'ar Azhar da ke kasar Masar, da ke neman samun fahimtar juna tsakanin musulmi da cewa, wannan babban ci gaba ne aka samua.
821864