Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran net a watsa rahoton cewa; a ranar sha biyar da sha shidda ga watan Murdad mai Kamawa ne na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Otawa na kasar Kanada za a gudanar da baje kolin kur'ani mai girma karo na biyu.Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Muslim Link ya bayanna cewa; wannan kasuwar baje kolin za a gudanar da ita ne a dalilin zagayowar Matan Ramadana mai albarka a cikin wannan wata mai albarka da daraja da musulmi ke kusantar Allah a cikinsa.Kuma wannan kasuwar baje kolin ta kwanaki biyu za afara da misalign karfe sha daua na rana a gogon kasar zuwa karfe takwas na dare kuma za a gabatar da shirye'shirye da dama daban daban da suka shafi kur'ani.
822112