IQNA

Husni Mubarak Ya Kasance yana TunzuraMalaman Masar Wajen Kafirta Shi'a

12:17 - July 13, 2011
Lambar Labari: 2153907
Bangaren kasa da kasa, babban malamin jami'ar Azhar mai bayar da fatawa a lokacin da yake zantawa da wasu daga cikin 'yan siyasa da kuma ma'aikatan yada labarai na kasar Masar ya bayyana cewa, tsohon shugaban mulkin kama karya na Husni Mubarak shi ne ya kasance yana tuzura malaman kasar wajen kafirta mabiya mazhabar shi'a.



Kamfanin dillanci labaran iqna ya habarta cewa,a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, Sheikh Ahmad Tayyib babban malamin jami'ar Azhar mai bayar da fatawa a lokacin da yake zantawa da wasu daga cikin 'yan siyasa da kuma ma'aikatan yada labarai na kasar Masar ya bayyana cewa, tsohon shugaban mulkin kama karya na Husni Mubarak shi ne ya kasance yana tuzura malaman kasar wajen kafirta mabiya mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar, da nufin gamsar da haramtacciyar kasar Isra'la.

Malamin ya ci gaba da cewa babbar manufar haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya ita ce ganin an samu rarrabuwar kawuna tsakanin mabiya addinin muslunci, wadanda suka hada sunna da shi'a kuma ta hanayar kawo rikici tsakanins za a iya haifar da baraka tsakanin muslumi, wanda kuma hakan na daga cikin ayyukan da Husni Mubarak ya daukar ma kansa yi.

Babban malamin jami'ar Azhar mai bayar da fatawa a lokacin da yake zantawa da wasu daga cikin 'yan siyasa da kuma ma'aikatan yada labarai na kasar Masar ya bayyana cewa, tsohon shugaban mulkin kama karya na Husni Mubarak shi ne ya kasance yana tuzura malaman kasar wajen kafirta mabiya mazhabar shi'a na kasar da ma na duniya baki daya.

824631
captcha