IQNA

A Cikin Watan Ramadan Mai Zuwa Ne Za A Bude Babban Masallacin Juma’a Na Strausburg

17:16 - July 16, 2011
Lambar Labari: 2155304
Bangaren kasa da kasa, a cikin ramadan mai alfarma d ake zuwa ne za abude wani babban masallaci najum’a abirnin Strausburg na kasar Faransa, tare da halartar malaman addini na kasar da kuma shugabannin cibiyoyin addini na birnin da ma wasu daga cikin manyan biran kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, a cikin ramadan mai alfarma d ake zuwa ne za abude wani babban masallaci najum’a abirnin Strausburg na kasar Faransa, tare da halartar malaman addini na kasar da kuma shugabannin cibiyoyin addini na birnin da ma wasu daga cikin manyan biran kasar ta Fransa.
Y akuma nakalto wani labarin daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar sharq akl-ausat an bayyana cewa, ana shirin bude wani baje koli na kayan muslunci da suka hada littafai da kuma abubuwan da ke nuni da matsayin ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba kan hakan.
826136

captcha