Bangaren kur’ani, babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin wasanni da motsa jiki na kasa ya aike da sakkonsa zuwa ga taron gasar karatun kur’ani mai tsarki da aka gudanar ta kasa baki daya, da kumahardar littafin nahjul balagah.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin wasanni da motsa jiki na kasa ya aike da sakkonsa zuwa ga taron gasar karatun kur’ani mai tsarki da aka gudanar ta kasa baki daya, da kuma hardar littafin nahjul balagah wanda ya samu halartar dalibai daga sassa na kasar baki daya.
Pira ministan kasar Malazia ya jaddada muhimmancin gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron bude gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na lebanonfiles an bayyana cewa, fadar Vatican ta mabiya addinin kirista da ke birnin Rom na kasar Italia za ta shiya gudanar da wani zaman taro na tattaunawa tsakanin mabiya addinai na duniya, wanda zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka hada dukkanin bangarorin ta yadda za a kara samun fahimtar juna tsakaninsu.
826666