IQNA

Al’umma Za Ta Tabbata Guda Daya Ce A Lokacin Bayyana Hujjar Ubangiji

17:07 - July 18, 2011
Lambar Labari: 2155976
Bangaren siyasa da zamantakewa, shugaban bangaren nazarin addinin muslunci na jami’ar Beheshti da ke nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa, al’umma za ta zama guda daya daidai da mafahumin aya a lokacin bayyana hujjar Allah a bayan kasa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklati daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, shugaban bangaren nazarin addinin muslunci na jami’ar Beheshti da ke nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa, al’umma za ta zama guda daya daidai da mafahumin aya a lokacin bayyana hujjar Allah a bayan kasa kamar yadda muminai suke bayyanarsa kamar yadda manzon tsira amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi alkawali.
cibiyar bunkasa ayyuka da suka danganci kur’ani mai tsarki a birnin Madina mai alfarma ta fara gudanar da wani shiri na samar da wani babban dakin ajiyar kayan tarihi, musamman ma wadanda suka danganci kur’ani mai tsarki, tare da hadin gwiwar cibiyar raya harkokin yawon bude ido da kuma adana kayan tarihi ta kasar baki daya.
Ya kara da cewa wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ra’y an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani kan mu’ujizar kur’ani mai tsarki da kuma adabi a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin ilimi da adabin musulunci ta kasa da kasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin na Aman.
A wani rahoton kuma an bayyana cewa a wani labari da aka nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na middle East Monitor cewa, ana Shirin bude hanyoyin karkashin kasa da yahudawan sahyuniya suka gina karkashin masallacin Qods mai alfarma, a lokacin da al’ummomin duniya gami da shugabannin larabawa suka yi gum da bakinsu kan wannan tabargaza ta yahudawan sahyuniya a wurare masu tsarki na al’umma.
826742
captcha