IQNA

Wasu Kafofin Yada Labarai Na Kokari Wajen Bayyana Akidar Zuhur

13:45 - July 19, 2011
Lambar Labari: 2156413
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin kafofin yada labarai na kasashen musulmi suna yin iyakacin kokarinsu domin bayyana akidar nan ta jiran bayyanar mai tseratar da duniya daga duhun jahilci da tsananin zalunci tare da umurnin Allah madaukakin sarki.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, wasu daga cikin kafofin yada labarai na kasashen musulmi suna yin iyakacin kokarinsu domin bayyana akidar nan ta jiran bayyanar mai tseratar da duniya daga duhun jahilci da tsananin zalunci tare da umurnin Allah madaukakin sarki, tare da tabbatar da dokokin ubangiji a bayan kasa.

Bayanin ya gaba da cewa rahotanni daga kasar Syria sun habarta cewa dakarun kasar na shirin shiga yankin Bukamal da ke kan iyakar kasar da kuma kasar Iraki, biyo bayan tashe-tashen hankulan da suka faru jiya a yankin.

Kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Syria ya habarta cewa, wasu masu dauke da makamai da suke kiran kansu 'yan adawa a kasar Syria, sun kai hari jiya kan ofisoshin 'yan sanda da ke garin Bukamal, inda suka kasha jami'an tsaro uku kuma suka kwashe tasrin makamai da ke wurin, sun kuma ta yin harbe-harbe daga kan rufin gidaje, da sunan yunkurin kawar da gwamnatin shugaba Bashar Asad, lamarin da ya tilasta dakarun kasar suka nufi yankin a yau domin tabbatar da doka da oda, tare da kare yakokin kasar da kasar Iraki.

Kimanin watannin hudu kenan da kasar Syria take ganin tashe-tashen hankula a wasu yankunan kasar, tun bayan da 'yan bindiga suka fara kai farmaki kan jami'an tsaro da ma fararen hula, gwamnatin Syria ta zargi kasashen yammacin turai da wasu daga cikin kasashen larabawa 'yan koren Amurka da shirya mata makarkashiya, lamarin da ta bayyana cewa ba zai yi nasara ba.

827192

captcha