Kamfanin dilalncin labaran iqna yahabarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shoura an bayyana cewa, mabiya addinin muslunci na birnin Luxambur na kasar faransa za su fara azumi a ranar karshe ta watan Yulin nan da muke ciki a matsayin ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma kamar yadda babba cibiyar kula da ayyukan muslunci ta yankin ta sanar.
Shugaban cibiyar ya dada cewa a kowane lokaci suna son su ga sun bi lamurra daidai ba tare da samun wata matsala ba kan dukkanin abubuwan da suka hada musulmi, a kan haka a wannan shekarar ma za su yi kokari su tafi tare da akasarin muslmi wajen daukar azumin watan Ramadan na wanan shekara.
Rahoton ya kara da cewa mabiya addinin muslunci na birnin Luxambur na kasar faransa za su fara azumi a ranar karshe ta watan Yulin nan da muke ciki a matsayin ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma kamar yadda cibiyar raya harkokin muslunci ta saba sanar da shirinta makonnin kafin watan.
827170