IQNA

An Gudanar Da Taron Girmama Daliban Kur'ani A Kasar India

19:54 - July 19, 2011
Lambar Labari: 2156603
Bangaren kur'ani, an gudanar da wani taro na girmama daliban kur'ani mai tsarki an kasar India da suka shiga gasar hauza da musulunci a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (AS) a cikin wannan mako.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, an gudanar da wani taro na girmama daliban kur'ani mai tsarki an kasar India da suka shiga gasar hauza da musulunci a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (AS) a cikin wannan mako da muke ciki.

A wani labar da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na ami an bayyana cewa, za a nuna wani mushafin kur'ani mai tsarki na kasar Mauritaniya da aka kira mushafin kasa mai suna Shakit, wanda za a kammala dukkanin ayyukansa daga nan zuwa karshen wannan shekara da muke ciki ta 2011.

Bayanin ya ci gaba da cewa an rubuta wannan kur'ani mai tsarki ne da salon rubutu na kasar d ake yin amfani da shi a hukumance, kuma a cikin wannan mako da muek ciki ne za a gyara bangare kashi uku bisa hudu na mushafin da aka kammala rubutunsa a birnin Nuwakshout fadar mulkin kasar.

Yanzu haka dai ana shirin nuna wani mushafin kur'ani mai tsarki na kasar Mauritaniya da aka kira mushafin kasa mai suna Shakit, wanda za a kammala dukkanin ayyukansa daga nan zuwa karshen wannan shekara da muke ciki kamar dai yadda ma'aikar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar.

827089



captcha