Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar alwatan da ake bugawa a kasar saudiyya an bayyana cewa, babbar cibiyar mabiya addinin muslunci da kuma malamai ta duniya za ta gudanar da wani zaman taro a birnin Alkahira na kasar Masar, domin tattauna muhimamn batutuwa da suka danganci musulmi a duniyarmu ta yau, da kuma fuskantar manyan kalu bale da suke gabansu.
A wani labarin kuma shugaban kasar Ivory Coast Alassane Oattara ya amince da kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan rikicin siyasar da kasar ta yi fama da shi wanda ya lakume rayukan mutane da dama.
A cikin wani bayani da aka fitar bayan kammala zaman majalisar ministocin kasar Ivory Coast a jiya a birnin Abijan, an bayyana cewa shugaba Ouattara ya amince da kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan abubuwan da suka faru bayn gudanar da zaben shugaban kasa, bayan da tsohon shugaban kasar ya ki amincewa da kayin da sha, lamarin day a jefa kasar cikin mummunan rikici, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kalla 3000, tare da tserewar wasu sama da miliyan daya daga yankunansu.
Tun kafin wannan lokacin dai masu bincike na kotun manyan laifuka ta duniya sun bayyana cewa, dukkanin bangarorin biyu masu goyon Lauren Bagbo, da kuma masu goyon bayan Alassane Ouattara sun tafka laifukan cin zarafin dan adam a lokacin rikicin. 829396