Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya samu daga shafin yanar gizo an bayyana cewa, ga dukkan alamu dai a daren yau ne za a kawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa akasar malazia tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na duniya, da suka hada da kasashen musulmi da na larabawa da ma wasu kasashe da ba su cikin kasashen muslmin duniya.
A ranar lahadin da ta gabata ce majalisar hadin gwuiwar kasashen yankin Tekun Fasha ta gudanar da taronta a birnin Riyadh babban birnin kasar Saudiyya don tattaunawa kan lamurran da suke gudana a yankin da kuma abin da suka kira tsoma bakin kasar Iran cikin lamurran cikin gidan kasashen larabawa. A sanarwar bayan taron da ya sami halartar ministocin harkokin wajen kasashen majalisar, kamar yadda suka saba yi ministocin sun bayyana damuwarsu dangane da abin da suka kira tsoma bakin Iran cikin harkokin cikin gidan kasashen Tekun Fashan.
Majalisar dai ta bayyana damuwar da Iran take nunawa dangane da irin dirar mikiyan da gwamnatin Bahrain bisa goyon bayan kasar Saudiyya suke yi wa mutanen kasar a matsayin tsokana suna masu cewa zanga-zangar da mutanen Bahrain suke yi wani makirci ne daga waje da nufin kifar da gwamnatin kasar sannan kuma sun nuna rashin amincewarsu da kiran da Iran ta yi wa kasar Saudiyya na ta fice daga kasar Bahrain din.
Abin da ko shakka babu cikinsa shi ne cewa damuwar da majalisar hadin gwuiwar kasashen Tekun Fasha take ciki dangane da guguwar sauyin da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afirka shi ne dalilin da ya sanya ta gudanar da wannan taro a kasar Saudiyya, to sai dai ta yi amfani da wannan batu na kasar Bahrain ne kawai don wasa da hankulan mutane da kuma neman mafita daga matsalolin da wadannan kasashe da gwamnatocinsu suke fuskantar na barazanar wannan guguwar sauyi.
To sai dai kuma a halin yanzu wasu 'yan siyasa da kafafen watsa labaran kasashen yammaci suna ta kokari wajen haifar da rikici da sabani tsakanin Iran da kasashen larabawan Tekun Fasha sakamakon wannan yanayi da aka samar. Don kuwa wadannan kasashen da ma wasu daga cikin kasashen larabawan sun dauki wannan lamari a matsayin makamin da za su yi amfani da shi wajen wasa da kwakwalan mutane daga fahimtar hakikanin dalilan guguwar sauyin da take faruwa a kasashen larabawan da kokarin da al'ummomin kasashen suke yi na kawar da gwamnatoci 'yan amshin shatan kasashen yammaci daga kasashensu ciki kuwa har da ita kanta gwamnatin kasar Bahrain din.
Abu ne da yake a fili cewa kasashen yammacin za su yi maraba da irin wannan matsaya da majalisar hadin gwuiwan kasashen Tekun Fashan ta dauka. Don kuwa ci gaba da yaduwar irin wannan juyin juya hali na mutane a kasashen larabawa musamman ma a kasar Bahrain wacce ta zamanto sansani na asali na sojan Amurka a Tekun Fasha lamari ne da zai tada hankalin kasar Amurka. Baya ga kare bakar siyasar Amurkan da wadannan gwamnatoci suke yi, har ila yau kuma wadannan gwamnatoci sun zamanto manyan masu sayen makaman kasar Amurkan ta yadda kididdiga ta tabbatar da cewa tsakanin shekara ta zuwa wadannan kasashe na tekun fasha su ne suka fi sayen makaman Amurka. Don haka ko da wasa Amurka ba za ta yi wasa wadannan kasashe su kubuce mata ba musamman a irin wannan lokaci da Amurkan take fuskantar matsalar tattalin arziki akasar ta Malazia.
829676