IQNA

Azhar Ta Hana Watsa Wani Fim Na Imamai Hassan Da Hussain (AS) Saboda Nuna Fusakunsu

12:46 - July 24, 2011
Lambar Labari: 2158876
Bangaren kasa da kasa, jami'ar Azhar ta kasar Masar ta aike da wata wasika ta gargadi ga tashar talabijin ta Nile sat a shirin da take da shi na watsa wani fim na Imamai Hassan da Hussain (AS) a cikin watan Ramadan mai zuwa, saboda nuna fusakunsu da aka yi a cikin fim din.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na masrwy an bayyana cewa, jami'ar Azhar ta kasar Masar ta aike da wata wasika ta gargadi ga tashar talabijin ta Nile sat a shirin da take da shi na watsa wani fim na Imamai Hassan da Hussain (AS) a cikin watan Ramadan mai zuwa, saboda nuna fusakunsu da aka yi a cikin fim din, wanda jami'ar take ganin cewa hakan ya sabawa koyarwar muslunci a nuna fusakun ahlul bait masu tsarki a cikin fina-finai.

Jami'ar Azhar dai ita ce jami'ar musulucni mafi girma da jimawa awannan zamani, kuma bangarori daban-daban da suke kula da lamurran fatawa da sa ido kan abubuwan da ake aikatawa da matsayinsu a cikin addnin muslunci, musamman ma abubuwan da suka danganci muslunci da musulmi.

Dangane da hakan jami'ar Azhar ta kasar Masar ta aike da wata wasika ta gargadi ga tashar talabijin ta Nile sat a shirin da take da shi na watsa wani fim na Imamai Hassan da Hussain (AS) a cikin watan Ramadan mai zuwa, saboda nuna fusakunsu da aka yi a cikin fim din wanda shi ne karon farko da za awatsa shi.

Kafin wanna lokacin dai an fina-finai masu masu a kasashen musulmi musamman ma a jamhuriyar muslunci ta Iran, inda aka saka haske a kan fusakun mutane masu tsarki, musamman ma limamai daga cikin ahlul bait (AS)

829883
captcha