Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hula da jama'a babbar cibiyar hada-hadar kasuwanci ta birnin Tehran an bayyana cewa, kwamitin hadin gwiwa tsakanin jamhuriyar muslunci ta Iran da kuma kasar Bosnia kan harkokin kasuwanci ya fara aiki a hukumance daga wannan mako da muke ciki, bayan kaddamar da shi tare da halartar jami'ai daga dukaknin kasashen biyu.
A nasa bangaren shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa a kodayaushe Iran tana baiwa hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa hadin kai.
Shugaban na jamhuriyar musulunci ta iran, Mahmud Ahamdi Nejad da ya ke maida martani akan shawarar da kasar Rasha ta gabatar na daukar matakai daki-daki domin kawo karshen cece-kuce akan shirin makamashin nukiliar Iran na zaman lafiya, ya ce: "Akodayaushe Iran tana aiki kafada da kafada da hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa."
Shugaba Mahmud Ahmadi Nejad ya yi kira ga bangarorin da ake tattaunawa da su akan shirin makamashin nukiliyar na Iran da su kawo karshen matakan siyasar da su ke dauka domin bude sabon shafi na aiki tare da Iran.
ministan harkokin wajen kasar Rasha Sargey Lavrov ne ya shaidawa takwararsa ta Amurka cewa da akwai bukatar a dauki matakai daki-dakai na warware batun makamashin nukiliyar Iran wanda zai kai ga dauke takunkumin da aka kakaba mata.
830301