IQNA

Masallacin Strausburg Zai Dauki Nauyin Karatun Kur'ani A Watan Ramadan

11:12 - July 25, 2011
Lambar Labari: 2159426
Bangaren kasa da kasa, babban masallcin birnin Strausburg na kasar Faransa zai dauki nauyin tarukan karatun kur'ani mai tsarki, wanda zai samu halartar mabiya addinin muslunci daga sassa daban-daban na birnin a cikin wannan wata mai alfarma.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mosque an bayyana cewa, babban masallcin birnin Strausburg na kasar Faransa zai dauki nauyin tarukan karatun kur'ani mai tsarki, wanda zai samu halartar mabiya addinin muslunci daga sassa daban-daban na birnin a cikin wannan wata mai alfarma, akmar dai yadda aka saba gudanarwa a kowace shekara.
A zaman taron kwamitin harkokin wajen majalisar dattijan Amurka jamian gwamnatin kasar sun bayyana rashin muhimmancin sanarwar da masu adawar kasar Yaman suka fitar a kwanan nan ta bayyana goyon baya akan cewa Majalisar Shugabanci ta Wucin Gadi da aka kafa a kasar ta rike ragamar gudanar da shugabanci. Wannan majalisa dai kungiyoyin matasa masu yunkurin kawar da gwamnatin Ali Abdullah Saleh ne suka kafa ta domin kawo karshen gwamnatin Saleh wanda yanzu haka ya ke kasar Saudiya domin jinya sakamakon wani harin da aka kai masa a kwanakin baya.
Tun kafin shugaba Saleh ya tafi Saudiya kasar Amurka bata mai da martanin a zo a gani ba a kan matakan da shugaban na Yaman yake dauka na murkushe masu zanga zanga da kashe mutane da kuma cin zarafi. A wani lokaci ma Amurkan tana nuna goyon baya wa shugaban kasar Yaman din, da hujjar cewa yan kungiyar Alkaida zasu sami karfi a kasar idan Ali Abdullahi Saleh ya sauka daga karagar mulki, saboda kawancen da yake da shi da Amurka akan abin da ta kira yaki da taaddanci.
830365

captcha