Bangaren kur'ani, da dama daga cikin masu duba baje kolin kur'ani mai tsarki da ake gudanawa a jamhuriyar muslunci ta Iran sun nuna matukar gamsuwarsu kan yadda koyarwar kur'ani ta bayar da gudunmwa wajen wayewar al'umma.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, mataimakin shugaban cibiyar da ke shirayawa da gudanar da baje kolin ya bayyana cewa, da dama daga cikin masu duba baje kolin kur'ani mai tsarki da ake gudanawa a jamhuriyar muslunci ta Iran sun nuna matukar gamsuwarsu kan yadda koyarwar kur'ani ta bayar da gudunmwa wajen wayewar al'umma, musamman a halin yanzu da al'ummomin musulmi da na larabawa suke mikewa domin nuna rashin amincewa da mulkin kama karya a cikin kasashensu.
Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin wadanda aka zanta da su sun bayyana matukar jin dadinsu dangane da gagagrumar gudunmawar da Iran take bayarwa wajen kara nusar da mutane kan muhimman abubuwan day a kamata su mayar da hankali kansu a wannan zamani.
Da dama daga cikin masu duba baje kolin kur'ani mai tsarki da ake gudanawa a jamhuriyar muslunci ta Iran sun nuna matukar gamsuwarsu kan yadda koyarwar kur'ani ta bayar da gudunmwa wajen wayewar al'umma a tsawon zamuna.
830963