Bangaren kasa da kasa, an tattauna batun kafa kwamitin kasa da kasa na lauyoyi musulmi a zaman da aka gudanar a birnin Makka mai alfarma, wanda ya samu halartar lauyoyi daga kasashen duniya daban-daban da nufin shiga kafar wando daya da masu cin zarafin musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labar da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an tattauna batun kafa kwamitin kasa da kasa na lauyoyi musulmi a zaman da aka gudanar a birnin Makka mai alfarma, wanda ya samu halartar lauyoyi daga kasashen duniya daban-daban da nufin shiga kafar wando daya da masu cin zarafin musulmi da musulunci a duniya, musamman ma dai acikin kasashen yammacin turai.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan mataki yana da matukar muhimamnci ga musulmi, dimin kuwa da dama daga cikin abubuwan da ake yi musu baya rasa nasaba da rashin daukar matakai na shari'a da suke yi, amma yiin hakan zai kara tabbatarwa masu tsanain kiyaya da addinin muslunci cewa musulmi ba wawaye ba ne kamar yadda suke tsammani.
An tattauna batun kafa kwamitin kasa da kasa na lauyoyi musulmi a zaman da aka gudanar a birnin Makka mai alfarma, wanda ya samu halartar lauyoyi daga kasashen duniya daban-daban da nufin shiga kafar wando daya da masu cin zarafin musulmi da addininsu a cikin kasashen turai.
831253