Bangaren kasa da kasa, Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah ya gabatar da wani jawabi na tunawa da kawo karshen yakin da ka yi tsakanin Hizbullah da Isra'ila, inda Allah ya baiwa hizbullah nasara kan yahudawan sahyuniya.
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, a rahotoon da ya nakalto daga sharing sadarwa na tashar talabijin ta Almanar an bayyan acewa, Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah ya gabatar da wani jawabi na tunawa da kawo karshen yakin da ka yi tsakanin Hizbullah da Isra'ila, inda Allah ya baiwa hizbullah nasara kan yahudawan sahyuniya, ayakin kwanaki 33 da Isar'aila ta kaddamar kan al'ummar Lebanon.
Bayanin ya ci gaba da cewa Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanan Sayyid Hassan Nasrullah ya ja kunnen HKI cewa kada ta kuskura ta shiga ruwan kan iyakar kasar Labanan domin satar man fetur da iskar gas din kasar.
Sayyid Nasrullah ya yi wannan kashedin ne a jawabin da ya yi a jiya a bikin tunawa da ranar da Hizbullah ta yi nasara a kan sojojin HKI a yakin da gwamnatin Sahyoniya ta kaddamar a kan kasar Labanan a shekarar 2006.
Sakataren na Hizbyullah ya kara da cewa duk wanda ya lalata albarkatun kasar Labanan to lallai za a lalata nasa albarkatun kasan, yana mai ishara ga gwamnatin HKI.
A bara ne dai gwamnatin Sahyoniya ta sanar da cewa ta gano isakar gas mai dumbin yawa a karkashin ruwa a tekun Meditaraniya, amma jamian gwamnatin kasar Labanan sun ce iskar gas din tana cikin yankin teku mallakin kasar Labanan.
832204