IQNA

Za A Bude Taron Baje Kolin Kur'ani Mai Tsarki Na Kasa Da Kasa Na 19

10:17 - July 28, 2011
Lambar Labari: 2161275
Bangaren kur'ani, za a bude baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya a karo na goma sha tara a babban masallacin juma'a na Imam Kohmeini (RA) da ke birnin Teran a jamhuriyar muslunci ta Iran, tare da halartar wakilan cibiyoyin kur'ani da madaba'antu da kuma jami'an gwamnati.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, za a bude baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya a karo na goma sha tara a babban masallacin juma'a na Imam Kohmeini (RA) da ke birnin Teran a jamhuriyar muslunci ta Iran, tare da halartar wakilan cibiyoyin kur'ani da madaba'antu da kuma jami'an gwamnatin kasar, wadanda suke taka gagarumar rawa wajen kara fadada ayyuka da suka danganci wannan bangare.

Taron buje wannan gagarumin baje koli dai zai fara daga karfe takwas na dare a yau, kumashugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad shi ne zai jagoranci bude wannan baje koli, sai kuma ministan ma'aikatar kula da harkokin al'adu, da babban jami'n ma'aikata mai kula da ayyukan da suka shafi kur'ani mai tsarki.

Baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya a karo na goma sha tara a babban masallacin juma'a na Imam Kohmeini (RA) da ke birnin Teran a jamhuriyar muslunci ta Iran, tare da halartar wakilan cibiyoyin kur'ani da madaba'antu da kuma jami'an gwamnati, hakan na daga cikin muhimamn abubuwan da ake gudanarwa akasar Iran domin kara raya harkokin kur'ani mai tsarki.

Sai kuma labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Benama an bayyana cewa, a dare na bakwai a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya da ake gudanarwa a birnin Kualalmpour na kasar Malazia, makaranta bakwai ne suk kara da juna da suka kunshi maza biyar da kumamata biyu a gasar da ake gudanarwa a karo na 53.

832823


captcha