Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda jama'a na cibiyar bunkasa harkokin aladu an bayyana cewa, a daidai lokacin da ake shirin shiga watan Ramadan mai alfarma, an gudanar da wata gasar harda da karatun kur'ani mai tsarki da ta kebanci matasa a tarayyar Nigeria a karami ofishin jakadancin jamhuriyar muslunc ta Iran da ke birnin Lagos cibiyar hada hadar kasuwanci ta tarayyar Nigeria.
Bayanin ya ci gab ada cewa an gabatar da jawabai a wajen wannan gasa ga mahalarta a lokacin da ake bude ta, daga cikin wadanda suka gabatar da jawaban kuwa hard a malaman adini da aka gayyata daga sassa daban-daba na tarayyar Nigeria, inda jaddada muhimamncin yin aiki da koyarwar kur'ani mai tsarki.
An nakalto wani rahoton kuma daga kamfanin dilalncin labarai na bernama an bayyana cewa, a dare na bakwai a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya da ake gudanarwa a birnin Kualalmpour na kasar, makaranta bakwai ne suk kara da juna da suka kunshi maza biyar da kumamata biyu a gasar da ake gudanarwa a karo na hamsin da uku a kasar wadda daya ce daga cikin kasashen gabacin Asia.
Daga cikin wadanda suka kai ga wannan mataki hard a 'yan kasashen Sudan, Viatnam, Thailand, Senegal, Srilanka da dai sauransu, lamarin da ya bayar da matukar mamaki, domin babu ko daya daga cikin kasashen da ta samu kaiwa zuwa ga mataki na karshe a wannan taro.
A dare na bakwai a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya da ake gudanarwa a birnin Kualalmpour na kasar , makaranta bakwai ne suk kara da juna da suka kunshi maza biyar da kumamata biyu domin neman kaiwa ga mataki na karshe a wanna gasa.
Kasar a dai tan taka gagarumar rawa ta fuskacin raya ayyuka na kur'ani da suka hada da shiriya tarukan addini da suke yin bahasi kan kur'ani da ilmomonsa, gami da irin wannan gasa da teke daukar nauyin shiryawa a kowace shekara.
832809