Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto da aka buga a shafin yanatr gizo na jaridar Al-riyad da ake bugawa a kasar saudiyya, da ke cewa daliban makarantun sakandare 500 ne da sukahardace kur’ani mai tsarki za agirmama ayankin Katif da ke gabacin kasar Saudiyya, wanda mafi yawan mazauna cikinsa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa ne a wannan rana.
Labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an sheda cewa, makarancin kur’ani mai tsarrki Sayyid Sadeq ya samu gagarumar karbuwa agasar karatun kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Kuwait a matsayi na kasa da kasa, inda ake gudanar da rana ta hudu bayan fara ta ranar juma’ar da ta gabata, inda daruruwan makaranta daga kasashen musulmi da na larabawa suke karawa da juna domin nuna irin baiwar da Allah madaukakin sarki ya yi musu.
Makarnaci ya samu kyakkyawar karbuwa daga su kansu makaranta da suke halartar wannan gasa daga kasashen duniya daban-daban musamman na musulmi da na larabawa, kamar yadda kwamitin shirya gasar ya nuna matukar gamsuwa da yadda yake yin amfani da salo na musamman wajen karanta littafin Allah mai tsarki, bayan kammala gasar dai za abayar da kyutuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo.
makarancin kur’ani mai tsarrki Sayyid Sadeq ya samu gagarumar karbuwa agasar karatun kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Kuwait a matsayi na kasa da kasa, inda ake gudanar da rana ta hudu bayan fara ta ranar juma’ar da ta gabata, inda daruruwan makaranta daga kasashen musulmi da na larabawa suke gogawa da junasu.
833419