IQNA

Watsa Fim Din Cin Zarafi Ga Iyalan Gidan Manzo Ya Saba Wa Fatawar Azhar

16:26 - August 04, 2011
Lambar Labari: 2165087
Bangaren kasa da kasa, watsa fim din da aka shirya domin zarafin iyalan gidan manzon Allah duk kuwa da jan kunnen da jami'ar Azhar ta yi kan hakan, ya sabawa fatawar babbar cibiyar muslunci ta kasar Masar baki daya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na g4me an bayyana cewa, watsa fim din da aka shirya domin zarafin iyalan gidan manzon Allah duk kuwa da jan kunnen da jami'ar Azhar ta yi kan hakan, ya sabawa fatawar babbar cibiyar muslunci ta kasar Masar baki daya da ma sauran kasashen musulmi da suke bin sahihin tafarkina sunna.

Wasu daga cikin tashoshin kasashen larabawa da suka hada da kasashen Masar, Saudiyya, Morocco, Lebanon Sudan sun fara nuna wannan fim da aka shirya domin cin zarafin iyalan gidan manzon Allah (SAWA) inda ake nuna fusakun Imamai biyu Hassan da Hussain (AS) da kuma Sayyid Fatima Zahra (AS) wanda jami'ar Azhar ta fitar da fatawar rashin halascn nuna wannan fim, domin tamkar cin zarafi ne ga iyalan gidan manzo.

Yin gaban kansu da wadannan gidanan talabijin na kasashen larabawa suka yi wajen watsa wannan fim, na tabbatar da cewa sun yi watsi da fatawar addinin muslunci da jami'ar Azhar ta bayar kan hakan, wanda kuma mabiya tafarkin iyalan iyalan gidan manzon Allah ba za su yi shiri kan hakan ba.

Fim din da aka shirya domin zarafin iyalan gidan manzon Allah duk kuwa da jan kunnen da jami'ar Azhar ta yi kan hakan, ya sabawa fatawar babbar cibiyar muslunci ta kasar Masar baki daya kuma manufar hakan ita ce kawo rikici tsakanin muslumi.

836541

captcha