Bangaren kur'ani, a daidai lokacin da aka fara gudanar da azumin watan Ramadan mai alfarma a dukkanin kasashen duniya inda musulmi suke rayuwa, an gudanar da wani zaman taro kan koyarwar kur'ani mai tsarki a birnin Jakarta na kasar Indonesia.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayanna cewa daidai lokacin da aka fara gudanar da azumin watan Ramadan mai alfarma a dukkanin kasashen duniya inda musulmi suke rayuwa, an gudanar da wani zaman taro kan koyarwar kur'ani mai tsarki a birnin Jakarta na kasar Indonesia babban birnin kuma fadar mulkin kasar.
Rahoton ya kara da cewa, mai kula da bangaren hulda da jama'a na wannan cibiya Paimum Abdulkarim ya bayyana an samu gagarumin ci gaba ta wannan fuska idan aka kwakwanta da shekarar da ta gabata, inda adadin abin da aka bayar ya lunka, domin kuwa a shekarar da ta wuce cibiyar ta bayar da abinci ne ga mutane dari biya a kowace domin yin buda baki.
Wannan babbar cibiyar musulmi da ke birnin Jakarta na kasar Indonesia tana daukar nauyin buda bakin mutane dubu daya a kowace rana marayu da kuma matafiya, domin samun falalar wannan wata mai alfarma na Ramadan, kamar yadda daya daga cikin jami'an cibiyar ya sanar a jiya.
836591