Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar Masar sun nuna matukar rashin jin dadinsu da nuna wani fim na cin zarafin limamai biyu jikokin manzon Allah (SAW) da wasu kafofin sadarwa suke yi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi da ake bugawa a kasar Masar an bayyana cewa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar Masar sun nuna matukar rashin jin dadinsu da nuna wani fim na cin zarafin limamai biyu jikokin manzon Allah (SAW) da wasu kafofin sadarwa suke yi a cikin wannan wata na ramadana mai alfarma, musamman ma a kasar ta Masar.
Daya daga cikin fitattun masana daga cikin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar masar Al-tahi Hashimi ya bayyana cewa, bisa ga fatawar da bangaren bincike na jami'ar Azhar ya bayar kan rashin halascin wannan fim, da kuma bayanin da daya daga cikin manyan malaman hauzar birnin Qom Ayatollah Abbas Ka'abi ya bayar, suna nan kan bakansu na rashin amincew da nuna wannan fm.
Da dama mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar Masar sun nuna matukar rashin jin dadinsu da nuna wani fim na cin zarafin limamai biyu jikokin manzon Allah (SAW) da wasu kafofin sadarwa suke yi a cikin kasar ta Masar da ma wasu kafofin talabijin na wahabiyawa.
838855