IQNA

Ofishin Allamah Fadlollah Da Malaman Saudiyya Sun Musunta Amincewa Da Watsa Fim Din Hasnain

10:39 - August 09, 2011
Lambar Labari: 2167665
Bangaren kasa da kasa, ofishin babban malamin addinin nan na kasar Lebanon marigayi Allamah Sayyid Muhammad Hussain fadlollah ya fitar da wani bayani da ke kore amincewarsa kan yada fim din Hasnain (AS) kamar yadda wasu malaman Saudiyya suka kore amincewarsu kan hakan.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tawafuq an bayyana cewa, ofishin babban malamin addinin nan na kasar Lebanon marigayi Allamah Sayyid Muhammad Hussain fadlollah ya fitar da wani bayani da ke kore amincewarsa kan yada fim din Hasnain (AS) kamar yadda wasu malaman Saudiyya suka kore amincewarsu kan hakan duk da hakan kuma tashoshin talabijin din Masar da wasu na kasashen larabawa na ci gaba da sakawa.

Tun bayan da tashar tauraron dan adam ta Nilesat da ke kasar Masar ta kudiri aniyar saka wannan fim da a cikinsa aka bayyana fusakun limaman shiriya Hassan da Hussai da Sayyida Zahra (AS) malaman addinin muslunci a ko'ina cikin fadin duniya da hakan ya hada da jami'ar Azhar, inda suka nuna rashin halascin wannan fim da aka shirya domin cin zarafin iyalan gidan manzon Allah (SAW) tare da hadin baki da makiya addini.

Babban ofishin babban malamin addinin nan na kasar Lebanon marigayi Allamah Sayyid Muhammad Hussain fadlollah ya fitar da wani bayani da ke kore amincewarsa kan yada fim din Hasnain (AS) kamar yadda wasu malaman Saudiyya suka kore amincewarsu kan hakan kamar dai yadda bayanai suka tabbatar.

Shugaban ofishin nasa ya ce a lokacin da Allamah yana raye, ya bayar da fatawar halascin bayyana fusakun manyan mutane na tarihi da addini, amma dole ne a kiyaye wasu muhimman abubuwa kan wannan lamari.

839390

captcha