Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto labari daga shafin sadarwa na yanar gizo da ke cewa tsarin gidan sarautar kasar Saudiyya zai rushe saboda kin yin gyara cikin harkokin mulkin kasar bayan da alumma suka nemi da a samara da sauyi amma mahukuntan gidan sarautar da suke bin turawan yamma ido rufe sun ki yin komai kuma masu gidansu yahudawa da sauran kasashen turai na ci gaba da yin shiri da bakunansu dangane da hakan.
Ibadar azumi ba aiki ba ne wanda ake gani kamar yin sallah ko aikin hajji, ita ibada ce ta kamewa daga barin wasu abubuwa a wani kayyaden lokaci a cikin wata daya, wato ramadan mai alfarma, inda mutum zai kame daga ci ko sha tun daga fitowar alfijin har zuwa bayan faduwar rana, kamar yadda wajibi ya kame daga dukkanin sha’wace-shawacensa, da kame bakinsa daga furta abubuwa na sabon Allah.
Azumi yan asirri a cikin rayuwar mutum ta addini da kuma ta ‘yan adamtaka, inda yakan natsar da ruhin mutum, da ba shi wani wani sabon yanayi na kusanci da Allah, a bangare guda kuma ya kan ladabtar da mutum ta hanyar dandana yunwa kishi, wanda hakan kan sanya mutum tunani kan marassa galihu da kuma halin da suke samun kansu a ciki, tare da tausaya musu da kuma taimaka musu, wanda a nan azumi ya zama wata hanya ta raya ruhin tausayi da kumanjin taimako a tsaknain mutane.
Gidan sarautar kasar Saudiyya zai rushe saboda kin yin gyara cikin harkokin mulkin kasar bayan da alumma suka nemi da a samara da sauyi amma mahukuntan gidan sarautar da suke bin turawan yamma ido rufe.
840320