IQNA

Hanyar Sanin Tattauna batun Hadisai A Hauzar Kur'ani Mai Tsarki

17:45 - August 10, 2011
Lambar Labari: 2168670
Bangaren ayyukan kur'ani, ana shirin gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan hanyoyin da za abi wajen samara da hanyar duba matsayin hadisai da tace su a hauzar kur'ani mai tsarki a taron baje koli na goma sha tara.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa an ambata cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan hanyoyin da za abi wajen samara da hanyar duba matsayin hadisai da tace su a hauzar kur'ani mai tsarki a taron baje koli na goma sha tara da aka saba gabatarwa a kowace shekara.

Watan ramadan wata ne na samun tsarki da kusanci da Allah, wata mai albarka da aka safkar da kur’ani a cikinsa, saboda haka mayar da hankali wajen karatun kur’ani da samun falalar hakan yafi yawa a cikin watan azumi fiye da sauran watannin shekara wannan aya za mu koyi cewa.

Wani mutum ya tambayi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gae shi cewa: shin Allah yana kusa da mu ne domin in kira shi a hankali, ko kuwa yana nesa ne domin in daga muryata a lokacin da nake kiransa? Sai wannan aya mai albarka ta dafka, inda take bayyana cewa Allah madaukakin sarki a koda yaushe yana kusa da bayinsa, wata ayar ma dake cikin surat Qaf tana ishara da cewa, shi ne ya fi kusa da bayanisa fiye da jijiyoyin wuyayensu.

Addu’a ba ta da wani wuri ko lokaci wanda za a ce dole sai nan kawai za a yi ta, a duk inda mutum ya samu kansa zai iya rokon Allah madaukakin sarki, kuma zai karba masa, yana tare da shi kuma yana saurarensa, amma shi watan ramadan yana da wani matsayi na musamman, domin kuwa addu’ar mai azumi karbabba ce.
840384
captcha